Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara yace gwamnatin Najeriya ta yi hasaran kudade masu dimbin yawa domin ta samar da wutan lantarki a kasa.
Yace a tsawon shekaru 18 da jam’iyyar PDP ta ke mulki an kashe sama da naira tiriliyan 2 don samar wa kasa wutan lartarki wanda hakan har yanzu bai haifar da da mai ido ba.
Yakubu Dogara ya fadi hakan ne a taron da ‘yan majalisar wakilai ta shirya domin matsalar rashin wutan lantarki da ake fama da shi a kasa Najeriya.
Ya kara da cewa majalisar ta shirya wannan taro ne domin jinjina wa wannan gwamnati akan kokarin da takeyi wajen ganin ta samar da isashshen wutan latarki a kasa Najeriya sannan da nemo wadansu hanyoyi da za’aiya amfani dasu domin samarda wutan lantarki a Najeriya.
Discussion about this post