An gudanar da addu’o’i domin Buhari a Kebbi da Bauchi

0

Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Bagudu ya jagoranci malamai da limaman jihar domin gudanar da addu’a ta musamman na neman Allah ya karawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari lafiya.

An gudanar da taron addu’an ne a babban filin idi da ke jihar.

Bayan haka kuma an yi irin hakan a garin Bauchi inda gwamnan jihar Mohammed Abubakar da sarkin Bauchi Rilwanu Adamu suka jagoranci addu’o’in.

A lokacin gudanar da wannan addu’o’i sarkin Bauchi yayi kira ga masarautun dake kasar Bauchi duka da su gudanar da irin wadannan addu’o’i ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya na kasar Ingila inda yake hutu da ganin likitoci kan lafiyarsa.

Yayi Magana da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje a makon da ya gabata a daidai ana gudanar da addu’o’i domin samun lafiyarsa a fidar gwamnatin jihar.

Buhari ya godewa ‘yan Najeriya da irin nuna damuwarsu akan lafiyarsa da sukeyi sannan ya ce yana samun karin lafiya akullum wayewar gari.

Share.

game da Author