Gidauniyar Dangote da gwamnatin jihar Kano sun gyara dakin haihuwa dake daukar mata masu ciki 90

0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje tare da hadin gwiwar gidauniyar Dangote sun gyara dakunan karban haihuwa mai daukar masu ciki 90 a asibitin Murtala da ke jihar Kano

Kakakin gwamnan jihar Kano Abdulaziz Mahmud ya ce dakunan karban haihuwan asibitin Murtalan ba ta taba samun irin wannan gyara ba tun da aka gina ta a shakarar 1924.

Bincike ya nuna cewa dakin karban haihuwan dake asibitin Murtala ita ce mafi girma a asibitocin kasar nan domin za ta iya karban haihuwan mata sama da 90 a rana.

Abubuwan da aka gyara a asibitin sun hada da Karo gadaje, samarda ruwan famfo, wadata asibitin da magunguna da dai sauransu.

A ranar Juma’ar da ta gabata gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya kai ziyara ginin asibitin da shugaban gidauniyar Dangote Aliko Dangote ta ke ginawa a jihar.

Za’a Kashe kudaden da ya kai naira biliyan 7 a aikin.

Ana sa ran idan an kammala asibitin zai iya zama mafi girma a arewacin Najeriya.

Share.

game da Author