Jarumi dan wasan fina-finan Hausa Adam Zango ya gaiyaci masoyan sa da ‘yan Najeriya da su fito su nuna masa yadda suke jin dadin lemon Amstel Malta ta hanyar hotuna ko bidiyo domin samun rakasa zuwa jihar Legas.
Kamfanin Amstel Malta sun gaiyaci Adam Zango da ya zo kamfanin na su da ke jihar Legas domin ganin yadda suke sarrafa lemon.
Ganin samun wannan daman, Adam shima yace toh bari ya nemi wadansu daga cikin masoyansa su tafi tare.
Yace zai zabi mutum biyar cikin masoyansa amma ta hanyar gasar hotuna da bidiyo.
“Kowa ya je ya dauko yadda yake jin dadin Lemon Amstel ta hanyar hotuna ko bidiyo sannan ya turo mini. Biyar da suka yi fice acikisu zan tafi dasu Legas domin ziyarar kamfanin Amstel Malta. Zan biya kudin komai da komai na mutum biyar din.” Inji Adam Zango.
Discussion about this post