Game da lafiya na babu wani abin tashin hankali Insha’Allah – Inji Buhari

2

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya godewa miliyoyin ‘yan Najeriya wadanda tun bayan tafiyarsa kasar lngila, suke ta aika masa da sakonnin fatan alheri da addu’o’in samun lafiya musamman a masallatai da majami’u dake kasa Najeriya.

Shugaba Buhari ya mika godiyarsa da irin damuwa, soyayya da kulawar da mutanen Najeriya suke yi masa ne a wata sanarwa da mai bashi shawara kan harkar yada Labarai, Femi Adeshina ya fitar.

Ya ce Buhari na kara tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa game da lafiyarsa babu wani abin tashin hankali Insha’allah.

Yayin duba lafiyarsa wanda ya saba yana yi duk shekara, a wannan shekarar likitoci sun shawarci Shugaba Buhari da ya dan dakata domin yin hutu mai dan tsawo don ya samu ya watsake ya kuma samu lafiya sosai wanda hakan ya sa Buhari zai kara tsawon kwanakin da zai yi a kasar.

Share.

game da Author