El-Rufai na gina sabuwar hanya daga filin jirgin saman Kaduna zuwa tashar jirgin kasa a Rigasa

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta na gina sabuwar hanya mai tsawon kilomita 6 daga filin jirgin saman jihar zuwa tashan jirgin kasa dake Rigasa a garin Kaduna.

Kwamishinan ayyukan jihar Ibrahim Uthman yace gwamnati ta yi hakanne saboda a sami saukin jigilan matafiya da ga filin jirgin saman Kaduna zuwa tashan jirgin kasan.

Za’a rufe filin jirgin saman Abuja domin gudanar da gyara wanda hakan ya sa gwamnati zabi filin jirgin saman Kaduna domin jigilan matafiya kafin a gama gyaran wanda zai dauki makonni 6 ana yi.

A dalilin haka ne gwamnatin Kaduna ta fara gina sabuwar hanya mai tsawon kilomita shida domin a kauce ma zagayen da da babu shi za’ayi kafin a kai tashar jirgin kasan daga filin jirginsaman Kadunan.

Mazauna unguwan Rigasa sun yaba wa gwamna Mal. Nasiru El-Rufai akan wannan kokari da yakeyi a jihar musamman a wannan lokaci.

Sunce matasan unguwan da basu da aikin yi yanzu sun sami abun yi domin ko ta ko ina aiki akeyi a jihar Kaduna.

Kwamishinan ayyukan jihar, Ibrahim Uthman ya kara da cewa bayan wannan aiki da gwamnatin jihar take yi akwai wasu manyan gadoji da akeyi a unguwanni Gwanin Gora da kewaye.

Share.

game da Author