Duk wanda yake yin amfani da addini wajen tada zaune tsaye, shaidan ne – Ahmed Maiyaki

0

Kakakin tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero, kuma jigo a jam’iyyar PDP a jihar Kaduna yayi kira ga shugabanni al’umma da na addini da su daina yin amfani da addini wajen ta da zaune tsayi a kasa Najeriya.

Maiyaki ya fadi hakanne yau a garin Kaduna lokacin da yake jawabi a wata ziyara da suka kai wa kungiyoyin Jama’atu da na Kiristocin Najeriya a Kaduna wanda wasu jami’an gwamnatin jihar suka shirya.

Maiyaki yace ya bi tawagar gwamnatin ne duk da banbancin jam’iyya da suke dashi domin nuna goyon bayansu akan ganin zaman lafiya ta dawo na dindindin a yankunan kudancin Kadunan da sauran sassan jihar baki daya..

Yace rashin zaman lafiya da yaki ci yaki cinyewa a jihar ya sa ayyukan cigaba da wannan gwamnati ta sa a gaba yana tafiyar hawainiya.

Ya kara da cewa ko da yake wannan gwamnati ta gaji rikicin ne amma kudaden da aka kashe zuwa yanzu da an kashe su wajen samarda kayayyakin more rayuwane da ba haka ba.

Ya roki mutanen jihar Kaduna da su zauna da juna lafiya.

Share.

game da Author