Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya cewa kasar sa za ta taimaka wa Najeriya da duk irin taimakon da zata bukata domin samun nasara akan yaki da Boko Haram da wannan gwamnati ta sa a gaba.
Donald Trump ya fadi hakanne a tattaunawa da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ta wayar tarho.
Buhari ne shugaba na farko da sabon shugaban kasar Amurka din ya fara magana dashi cikin Shugabannin kasashen Afrika.
Ya jinjina wa Buhari akan nasaran da ya samu wajen kwato ‘yan matan Chibok 24 cikin wadanda Boko Haram suka sace a makarantar Sakandaren dake Chibok.
Bayan haka kuma Trump ya gaiyaci Buhari Kasar Amurka a duk lokacin da ya shirya.
Buhari ya yi tattaunawarne daga kasar Ingila inda yake ci gaba da hutunsa da duba laciyarsa.
Discussion about this post