Da jam’iyyar PDP ta so da ta hana kafuwar APC – Inji Ahmed Makarfi

0

Shugaban jam’iyyar PDP bangaren Makarfi, Sanata Ahmed Makarfi yace duk da cewa jam’iyyar PDP na da karfin iya hana kafuwar jam’iyyar APC a wancan lokacin bata yi hakan ba sai gashi su yanzu ana yin amfani da matakan iko domin muzguna musu.

Makarfi ya fadi hakanne bayan taron jam’iyyar wanda ta yi yau a Abuja.

Yace abun da ya faru dasu ya faru a garin Fatakol sannan gashi ya faru anan kuma. Ya ce ba ya zaton irin wannan muzguna musu da ake yi ya kare kenan, za’a ci gaba.

Makarfi yace yana da yakinin cewa kotun koli za ta yi adalci a shari’ar su da suka kai gabanta.

A nashi bayanan, gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose ya yi tir da abun da jami’an tsaro suka ka yi musu na hana su yin amfani da dakin taro na ICC da ke Abuja ba.

Shi kuma Jerry Gana yace a ganinsa ba a yi musu adalci ba a hukuncin da kotun koli ta yanke saboda haka ne yasa gabadayansu suka amince da su daukaka karan zuwa kotun koli.

Share.

game da Author