Wani likita da ya kware a harkar cututtukan da ya shafi mata (Gynaecologist), Adewole Akintoyose ya shawarci su da su yawaita cin kayan lambu da ya hada da ganyayyaki da kayan itatuwa.
Likita Adewole yace yawaita hakan zai kare su daga kamuwa da ga cutar da ke yin lahani ga mahaifa mai suna ‘endometriosis’ a turanci.
Adewole ma’aikacin asibitin St. Leo da ke Lekki , jihar Legas.
Likitan ya yi bayanin cewa shi cutar ‘endometriosis’ yakan fito ne kaman kurji a gaban mace in a yake la’anta kwayayen mace, mahaifa da maran ta.
Likitan yace cutar na kawo rashin haihuwa saboda ya fi kama mata ‘yan shekara 25 zuwa 40.
Ya kara da cewa cutar bata nuna alamu a jikin mace amma akan gane cutar idan mace na yawan jin zafi ko radadi lokacin da take al’ada, yawan ciwon mara, jin zafi yayin da mace ke saduwa da namiji, rashin haihuwa, yawan gajiya, jin zafi yayin da take fitsari da kuma sauransu.
Likitan ya ce idan ba a nemi maganin cutar da wuri ba yakan rikide ya zama cutar dajin dake kama mahaifar mace.
Ya ce rashin haihuwa da wuri, fara gani jinin haila da wuri, daina haihuwa a lokacin da ya kamata na daga cikin alamun kamuwa da cutar.
Ya shawarci mata da su rage cin naman shanu domin shima yana iya kawo cutar.
Daga karshe yace ana warkewa daga cutar ne idan akayi wa macebn da ta kamu dashi fida da kuma shan maganin.