Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi wa sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa Hajiya Aminatu Mai Babban daki.
Buhari ya kira sarkin Katsina din ne yau daga birnin Landan.
Jiya Asabar ne Allah yayi wa mahaifiyar sarkin Katsina Hajiya Aminatu Mai Babban daki rasuwa.
Ta rasu ne bayan tayi fama da rashin lafiya sannan ta bar ‘ya’ya tara cikin su akwai sarkin Katsina
Abdulmumini Kabir Usman.
Anyi jana’izan Hajiya Aminatu yau lahadi a Katsina.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya na kasar Ingila inda yake hutu da ganin likitoci kan lafiyarsa.
Yayi Magana da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje a makon da ya gabata a daidai ana gudanar da addu’o’i domin samun lafiyarsa a fidar gwamnatin jihar.
Buhari ya godewa ‘yan Najeriya da irin nuna damuwarsu akan lafiyarsa da sukeyi sannan ya ce yana samun karin lafiya akullum wayewar gari.