Buhari ya gode wa ‘yan Najeriya

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace ya na mika godiyarsa ga ‘yan Najeriya saboda addu’o’I da suke ta yi masa tunda ya tafi kasar Ingila.

Buhari ya fadi hakanne a shafinsa na Twitter inda yace yana mika godiyar sa ga mutanen Najeriya, Musulmai da Kiristoci akan irin addu’o’in da suke ta yi masa tun bayan barin sa kasa Najeriya.

Ya mika godiyar sa ga shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki, Kakakin majalisar Wakilai Yakubu Dogara da Sanata Ahmad Lawal saboda ziyara da suka kai masa a kasar Ingila domin duba lafiyarsa.

Saraki yace ya ji dadin yadda ya ga Buhari kuma hakan ya tabbatar masa da cewa lallai yana cikin kuzari.

Share.

game da Author