Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo yace shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai bashi kunya ba tun da ga ranar da ya hau kujeran mulkin kasa Najeriya har zuwa yanzu.
Obasanjo yace a sanin Buhari da yayi tuntuni ba mutum bane da yake da amsoshi sosai ga yadda za’a bunkasa tattalin arzikin kasa, amma yayi matukar canzawa yanzu domin ana ta samun nasarori akan hakan a kasa Najeriya.
Ya ce dole a yabi Buhari saboda nasarorin da ya samu musamman na yaki da cin hanci da rashawa da sauransu.
Ya kara da cewa Buhari yayi abin azo a gani a tsaon kwanakin da yayi yana shugabancin kasa Najeriya.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da mara masa baya domin samun nasara akan abinda ya sa a gaba na gyaran Najeriya.