Babbar asibitin koyarwa da ke Ibadan wato UCH za ta fara taimakawa masu dauke da cutar daji, cutar shanyewar sashen jiki da kuma sauransu da magungunar da zai taimaka musu wajen gina garkuwan jikinsu , wato bitamin.
Shugaban asibitin Temitope Alonge ne ya yi bayanin hakan a garin Ibadan jiya lahadi.
Yace wannan asibiti zai zama shine na farko da zaifar bada irin wannan taimako.
Ya ce asibitin zai hada kai da wadansu asibitoci dake kasar turai mai suna ‘ActivLife Infusion Clinic’ domin su taimaka wa mutanen da ke dauke da irin wannan cututtukan.
Ya ce asibitin za ta bada magugunan da za su taimakawa marasa lafiya da garkuwan jikinsu ta yi rauni domin kara mata karfi saboda su sami kuzari a jikinsu sannan kuma za su dauki kwararen likita guda daya da kuma malaman asibiti biyu wato ‘Nurses’ domin kula da mutanen da ke dauke da irin wadannan cututtuka a asibitin.