Bayanai akan cutar daji 6 da mutane ke yawan fama da su da matakai 6 domin samun kariya daga su

0

Wani kwararren likitan kula da masu dauke da cutar daji Debo Omikunle ya yi kira ga ‘yan Najeriya akan mahimmancin wayar da kan juna game da cutar daji.

Likita Debo yace bincike ya nuna cewa a kowani shekara akalla mutane miliyan 12.7 ne suke kamuwa da cutar daji dabam dabam inda miliyan 7 daga ciki ke rasa rayukansu ta dalilin cutar.

Ya fadi haka ne a taron zagayowar ranar cutar daji ta duniya wanda akeyi a kowace ranar 4 ga watan Faburairu shekaran..

Likitan ya yi bayani akan cutar dajin da mutane musamman ‘yan Najeriya su ka fi fama da shi da kuma alamun da yake nuna wa idan mutum ya kamu da cutar sannan kuma ya fadi hanyoyin da za’a iya bi domin samun lafiya ko kukuma guje ma cutar.

1. Cutar dajin da ke kama nono;

Cutar dajin da ke kama nono na kama nonon maza da mata kuma yana daya daga cikin cututtukan da ke kashe mutane a kasan Najeriya.

Likita yace ce cutar dajin da ke kama nono shine mafi saukin ganewa domin cutar na nuna alamu kamarsu kunburin nono,fatar nonon ta canza kala, nono zai dunga fitar da ruwa da kuma sauransu.

2. Cutar dajin da ke kama ‘ya’yan golayen namiji wato prostate cancer kenan a turance;

Wannan cutar ta fi kama bakaken maza a duniya wanda ta dalilin haka ya sa maza da dama suka rasa rayukansu kuma har yanzu ba’a gano dalilin hakan ba domin baya nuna alamu a filin.

Likitan yace ana gane cutar ne idan ta kama namiji domin yana hana fitari yadda ya kamata, sannan kuma mutum ba ya kan iya yin fitsari ko tsayar da ita.

Likita ya shawarci maza da su yawaita zuwa yin gwaji musamman idan suka fara jin ba dai dai ba a mafitsaransu.

3. Cutar dajin dake kama dubura ;

Likita ya ce alamun cutar sune fitar da jini ta duburan, yin bayan gida tare da Ana ganin jini, jin zafi a kasan cikin mutum, rama da kuma sauran su.

Ya kuma ce irin wannan cutar dajin ba a iya gane shi da wuri domin haka ya shawarci mutane da su garzaya asibiti domin yin gwaji.

4 – cutar dajin dake kama mahaifa

Likita ya yi bayani akan abubuwan da ke kawo cutar dajin dake kama mahaifar mace kamar su shan kwayan maganin bada tazaran haihuwa, yin juma’I na farko ga ‘ya mace, haka kuma idan mace ta daina haihuwa shima yakan zama sanadi.

Likita ya ce ana iya warkewa daga cutar idan an gano cutar da wuri ta hanyar yin gwaji.

5. Cutar dajin dake kama huhu;

Likita yace wannan irin cutar dajin ta fi kama masu zukar taba sigari kuma ita ma ba’a iya gano ta da wuri sai ta kama mutum sosai kafin za’a gane cewa itace take damunsa.

Alamun da ake iya gane cutar shine yawan tari, cuwon kirji, canji a muryan mutum, kamuwa da cutar huhu, karacin nunfashi da kuma sauran su.

6. Cutar dajin dake kama Koda;

Likita ya ce ba a gane irin wannan cutar da wuri a jikin mutum domin cutar ba ta nuna alamu wanda za a iya gane wa da wuri.

Ya kuma ce alamun da cutar ke nuna wa bayan ta kama mutum sosai shine yi fitsari da jini, yawan gajiya a jiki, rama, kunburin tafin kafa da kuma sauran su.

Ya ce gwaji ne kawai zai sa a gano cutar kafin ta yiwa mutum lahani a jiki.

Share.

game da Author