Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta doke Athletico Madrid da ci 2 da 1 a wasan laliga na kasar Spain.
Barcelona ta Jefa kwallon ta na farko ne ta hannun dan wasanta Rafinha bayan an dawo hutun rabin lokaci. Jim kadan bayan haka sai dan wasan Athletico Madrid Diego Godin ya ramo kwallon a cikin minti 74.
Shahararren dan wasan Barcelona Leo Messi ya Jefa kwallo ta biyu minti uku kafin cikan lokaci.
Barcelona na saman kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da maki 54 ita ko da yake Madrid na da kwantan wasanni biyu.