Sani Aliyu kwararren likitane wanda ya kware akan kula cututtukan dake karya garkuwan jikin dan Adam.
Ya sami digirinsa na farko ne a jami’ar Ahmadu Bello inda bayan kammalawa ya fara aiki da asibitin dake fadar shugaban kasa a Abuja.
Bayan haka Likita Sani ya tafi kasar Amurka domin kara karatu akan aikin likitanci a shekarar 1998 a jami’ar Cambridge inda ya kware akan cututtukan dake karya garkuwan jikin dan Adam sannan ya yi aiki a asibitin jami’ar Cambridge din har na tsawon shekaru 10.
An nada sani Aliyu shugaban hukumar NACA ne a watan Nuwamban shekara ta 2016.
A hira da yayi da gidan Jaridar PREMIUM TIMES ya bada bayanai akan aikinsa da irin matakan cigaba da hukumar za ta kirkiro domin samun nasara akan hakan.
PT: Menene ra’ayin ka akan amfani da kayan gwajin cutar kanjamau kuma za’a iya shigowa da su kasa Najeriya domin mutane su yi amfani dasu don sanin matsayin su?
ALIYU: Shigo da kayan gwajin cutar kanjamau cikin kasa Najeriya nada kyau domin hakan zai taimaka wa mutanen da suke da fargaban zuwa asibiti yin gwaji sanin matsayinsu akan cutar kanjamau.
Duk da haka ina ba mutane shawaran cewa bayan ka gwada kanka da duk da haka ka garzayar asibiti domin samun sahihiyar sakamakon matsayin sa akan cutar.
PT: Me zaka ce game da sanarwan da hukumar NACA ta yi akan cewa kasa da kashi 10 na mutanen Najeriya kawai ne suka amince da yin gwajin cutar kanjamau?
ALIYU: A yanzu haka akwai rata sosai game da yadda mutane ke amincewa da yin gwajin cutar kanjamau domin mafiyawan mutane musamman matasa da kuma matan da suke dauke da juna biyu na tunanin cewa akwai maganin cutar kanjamau wanda zai taimaka wa rayuwar mutum ko da ya kamu da cutar soboda haka basa neman kare kansu daga cutar. Misali a shekarar 2015 adadin mutanen da suke da cutar kanjamau yakai miliyan 7.7.
Kamata ya yi a kowane lokaci mutane su yi kokarin sanin matsayin su akan cutar kuma idan mutum ya kamu ya kokarta ya dinga shan magani saboda hakan yana taimakawa wajen rage yaduwar cutar.
PT: Ta yaya kuke samun yawan adadin mutane da suke dauke da cutar kanjamau?
ALIYU: A gaskiyan lamarin shine bamu da ingantacciyar hanyar da muke samun labara akan adadin yawan mutanen da suke dauke da cutar kanjamau domin suna da yawa amma muna kokarin shigo da dabaran amfanin da naura mai aiki da kwakwalwa domin hakan zai taimaka mana wurin samun sahihiyar adadin yawan mutanen da suke dauke da cutar kanjamau a kasar gaba daya.
PT: Me zaka ce akan dogarar da kasa Najeriya ta ke yi wajen samun agaji domin yaki da cutar kanjamau daga kasashen waje?
ALIYU: Har yanzu kasa Najeriya na dogara akan agajin da kasashen waje ke bata duk da haka gwamnatin Najeriya ta kara kason kudaden da take warewa domin kawar da cutar kanjamau a kasan. Misali daga shekarar 2013 zuwa 2014 gwamanti ta kara kason kudaden da take warewa daga kashi 18 bisa 100 zuwa kashi 27 bisa 100.
Gwamnati ta kula cewa nauyin kawar da cutar kanjamau daga kasan ya yi mata yawa soboda haka ta ke kokarin hada karfi da karfe da sauran sassan gwamnati, ma’aikatan kiwon lafiya, hukumar NACA da kuma suransu domin ta ga ta cimma burinta.
PT: Me zaka ce game da rashin magungunan cutar kanjamau da Najeriay ke fama da shi kuma menene hukumar NACA take yi a kai?
ALIYU: Akwai tsarin da muke bi domin samar da magungunan cutar kanjamau kuma hukumar NACA ba a bar ta a baya ba. kamar yadda na fada da faro cewa abokan mu na kasashen waje su ke kawo mana magungunan cutar kuma muna aiki da su sau da kafa domin mu ga cewa asibitocin da ka bukatar magaungunan sun wadatu.
Bayan haka mu na kokarin gyara ma’ajiyar magani dake jihar Legas domin kawar da matsalolin da aka yi fama da su a shekarun baya kamar lalacewar magunguna wanda zai taimaka wajen samar da magungunan a kan lokaci. Sai dai muna rokon mutanen da suke dauke da cutar da su adage da shan magungunan yadda ya kamata.
PT: Ta yaya hukumar NACA ta ke sanin cewa mutanen da ke dauke da cutar kanjamau ne ke samun magungnan cutar?
ALIYU: Muna da tabbacin cewa mutanen da ke bukatar maganin cutar kanjamau na samun magunguna yadda ya kamata domin tsarin da ake bi a mafi yawan asibitoci shine da zaran aka gwada mutum kuma aka gano yana dauke da cutar nan da nan zai a yi masa rajista domin ya fara karban magani ba tare da an jirashi ya yi tunani ba.
PT: Wace shawara za ka bawa mutane game da gwaji da kuma karban maganin cutar kanjamau?
ALIYU: Shawarar da zan bada shine idan mutum ya san ya na dauke da cutar kanjamau toh ya kamata ya fara shan magani saboda hakan zai taimaka masa wajen cigaba da rayuwarsa kamar wanda bashi da cutar sukeyi.
Bayan haka kada mutane su bari ana rudansu cewa akwai maganin warkar da cutar a wurin malaman gargajiya domin babu kuma idan ana neman Karin bayanin akan cutar za a iya kiran layin wayar tarahon mu a laba kamar haka; 6222. Za’a iya kiran lambar wayar daga karfe 8 na safe zuwa 8 na yamma domin Karin bayani.
PT: Me nene dalilin dagewa da kuya akan cutar kanjamau?
ALIYU: Dalilin dagewar mu shine bincike ya nuna cewa cutar kanjamau ta fi kama samari wanda ko wace kasa ta san cewa su ne garkuwar tattalin arzikin kasar idan dai kasan na son ta ci cigaba.
Dalili ta biyu shine domin cutar kanjamau na kashe gaban dan Adam.
PT: Me zaka ce akan yadda ya kamata a dinga yin gwaji wa mutumin da ke dauke da cutar kanjamau?
ALIYU: A gaskiya ya danganta da jikin mutum domin bayan mutun ya gano yana dauke da cutar kuma yana shan magani kamata ya yi ya dinga yin gwaji bayan kowace wata 6 domin hakan zai sa a gane ko garkuwan jikin shi na kara karfi.
PT: Wasu nasarori ne hukumar ta samu game da rage yaduwar cutar kanjamau tsakanin uwa da kuma dan dake cikinta?
ALIYU: Da farko shawar da zan ba matan da suke dauke da juna biyu shine su yi kokarin garzayawa asibiti domin sanin matsayin su game da cutar.
Bincike ya nuna cewa matan da suke samnu kula ta fanin kare ya’yansu da ga kamuwa da cutar shine kashi 30 bisa 100 ne kawai amma kokari mu ke yi domin hakan ya karu zuwa kashi 90 bisa 100 ta hanyar karban maganin da aka fi sani da suna ‘Prevention of Mother and Child Transmission PMTCT’ domin kare yara jirajirai a mayan asibitoci da kuma cibiyoyin kiwon lafiya a kasa.
PT: Bincike ya nuna cewa wasu cikin mutanen da suke dauke da cutar kanjamau na biyan kudi kafin su karbi magani me zaka ce akan haka?
ALIYU: A ra’ayina kamata ya yi duk masu dauke da cutar kanjamau su karbi maganin a kyauta domin abokan mu na kasashen waje suke kawo mana magungunan kyauta kuma bada maganin a kyauta shine kadai hayar da zata iya rage yaduwar cutar a kasa Najeriya.
PT: Menene dalilin da ya sa hukumar NACA ta kasa kafa ofisohin hukumar a shiyoyin kasar nan?
ALIYU: Hukumar NACA ta gane mahimmancin haka amma dalilin da ya sa muka kasa kafa ofisoshin shine matsalar karancin kudi da hukumar ke fama dashi musamman wanda take bukata domin gudanar hakan.
A yanzu haka ba za mu iya tambayan kudaden da ga wurin gwamnati ba domin gwamnati ta riga ta gama da kasafin istimatin kudin shekarar bana amma muna kokarin ganin cewa gwamnati ta hada da namu bukatun a cikin kasafin istimatin kudin shekarar 2018.
PT: Ta yaya rashin kafa kwamitin amintattu na hukumar NACA ta shafi ingancin aiyukan ku musamman ta bangaren kara wa ma’aikata girma da kuma horar da mayan ma’aikata?
ALIYU: Hukumar NACA tana da kwamitin da nauyin hukunta ma’aikata duka ta rataya akan ta kuma kwamitin ce take zama tana tantance sunayen ma’aiktan da suka cancanci Karin girma, saboda haka rashin kafa wannan kwamiti na hukumar bai hana mu aikin da ya kamata mu yi ba.