Minister sifurin jirage sama, Hadi Sirika yace babu ruwan mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo kan canje-canjen da akayi a ma’aikata kula da sifurin jeragen sama taa kasa.
Minista Sirika ya sanar da sauke duka darektocin hukumar su tara in da daga baya aka dawo da guda biyu daga cikin su ranar Juma’ar makon jiya.
Yace wadansu kafafen yada labarai suna fadin cewa wai dalilin ziyarar mataimakin Shugaban Kasa filin jirgin saman Legas ne yasa akayi wadannan canje-canje, Hadi sirika yace ba haka bane.
An gano cewa lallai na bukatan gyara a hukumar ne wanda ya sa dole a gudanar da irin wannan sauye-sauye a ma’aikatar.