Ba zan dawo Najeriya ba sai likitoci sun gamsu da lafiya ta – Inji Buhari

3

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace ba zai dawo kasa Najeriya ba sai likitocin da suke kula da shi a kasar Ingila sun ce sun gamsu da lafiyarsa.

Buhari ya fadi hakanne a wasikar da ya rubuta ma shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki domin sanar da majalisar neman karin kwananki domin gudanar da gwaje gwajen akan lafiyarsa a can kasar na Ingila.

Gidan jaridar PREMIUM TIMES ta samu cikakkiyar wasikar da Buhari ya tura wa majalisar domin sanar musu da hakan.

Buhari ya tafi hutu kasar Ingila inda yayi amfani da hakan domin duba lafiyarsa.

Bayan kwanankin da ya dauka sun cika, ya rubuto wa majalisar kasa domin neman karin kwanaki ya ci gaba da zama a kasar har sai likitocin da suke duba shi sun amince masa da ya dawo kasa Najeriya.

Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne yake ci gaba da zama a kujeran mulki na wucin gadi har zuwa dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Karanta Labarin a shafin mu na turanci a nan: http://wp.me/p2LdGt-W4i

Share.

game da Author