Ba zan bari Boko Haram ta dawo Jihar Kogi ba – Inji Yahaya Bello

0

‘Yan kungiyar Boko Haram sun fara dawo wa jihar Kogi saboda fatattakarsu da sojojin Najeriya sukeyi a yankin Arewa Maso Gabas.

Gwaman Jihar Kogi Yahaya Bello ne ya fadi hakan a taron samar da tsaro da aka yi yau a garin Abuja.

Gwamnan yace ko jiya Sojoji sun kama wadansu ‘yan kungiyar book Haram su hudu a jihar.

Yahaya Bello yace idan har jihar suke so su dawo da zama toh su sani sunyi kuskure domin a shirye yake da ya kora su.

Yace gwamnatinsa za ta hada hannu da sojojin Najeriya domin ganin cewa basu sami abin da suke so ba a jihar.

A jawabinsa Sarkin Musulmi, Abubakar Sa’ad ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ci gaba da kokarin da takeyi domin kakkabe sauran mafakar kungiyar a yankin Arewa Maso Gabas.

Share.

game da Author