Ba za mu goyi bayan zanga- zangar da Tuface ya shirya ba – Kungiyar Mawakan jam’iyyar APC

0

Shugaban kungiyar mawakan jam’iyyar APC Haruna Ningi ya ce kungiyarsa ba ta goyon bayan zanga-zangar da mawaki Tuface ya shirya zai yi a karshen makon nan ba.

Tuface ya shirya wata zanga-zanga domin nuna bacin ransa da kira ga gwamnati da ta kawo wa mutane dauki akan irin wahalar da ake fama dashi a a kasa Najeriya.

Kungiyar ta ce tana da tabbacin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gyara kasa Najeriya sannan tayi korafin cewa ko a lokacin da ya hau karagar mulkin kasa Najeriya, komai na gab da rugujewa ne.

Kungiyar tace ta na goyon bayan wannan gwamnati kuma ta na da yakinin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta gyara kasa Najeriya.

Haruna Ningi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri da dan wahalar da aka shiga cewa an kusa fita InshaAllahu.

Ya ce kungiyar sa ba za ta shiga zanga-zangar ba.

Share.

game da Author