Ba mu ji dadin tafiya gaida Buhari ba tare da mu ba – Inji ‘Ya’yan Jam’iyyar PDP a majalisa

0

Ya’yan jam’iyyar PDP a majalisar tarayya sun koka da yadda aka yi musu saniyar ware wajen tafiya gaida Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kasar Ingila.

Shugaban marasa rijaye a majalisar Wakilai Leo Ogor yace sam bai ji dadi ba yadda aka nuna musu wariya wajen zaben wadanda suka tafi ziyarar Buhari.

Yace ko da mataimakin shugaban majalisar dattijai ne ay da an hada dashi a tawagar kawai sai aka tsallakeshi aka tafi da shugaban masu rijaye a majalisar dattijai, Ahmed Lawan.

Leo ogor yace ko dayake sun ga Buhari ya na dariya da bakin nasa wanda hakan ya musu dadi amma duk da haka ba da yawunsu aka tafi ziyarar ba.

Wata majiya daga ofishin mataimakin shugaban majalisar dattijai Ike Ekweremadu ya sanar mana cewa shi kansa bai san da tafiyar ba.

Daga karshe Leo Ogor yace tafiyar shugabannin majalisar Tarayya din tafiya ce ta son kai kuma a sani ba da yawun su bane sukayi wannan tafiya.

Wani dan majalisa kuma dan jam’iyyar PDP yace shi bai ga laifin ziyarar da shugabannin majalisar sukayi ba na zuwa kasar Ingila din domin duba shugaban kasa.

Dan majalisan mai suna Nicholas Osai daga jihar Delta yace ai su kansu shugabannin majalisar basu suka zabi kansu ba, ‘yan majalisar ne suka zabe su saboda haka ko da sun tafi da sunan wakilcin majalisar ne ya yi daidai.

Share.

game da Author