Sanannen attajirin nan kuma jigo a jam’iyyar PDP daga jihar Anambra Sanata Andy Uba ya canza sheka zuwa jam’iyyar APC.
Sanata Uba ya sanar da hakanne yau a mazabarsa ta Uga, dake karamar hukumar Aguata, jihar Anambra.
Andy Uba y ace ya canza shekar ne ganin cewa abokanansa ‘yan siyasa musamman daga jihar duk suna Jam’iyyar APC din Kamarsu Chris Ngige da George Muoghalu.
Bayan haka y ace yanzu dai ya gano cewa Jam’iyyar APC ta na da hangen nesa da irin manufofin da yake bukata domin kawo ma yankinsa cigaba mai amfani.
Akalla sanatoci hudu ne a ‘yan kwanakinnan suka canza scheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.
Yanzu dai jam’iyyar APC na da sanatoci 65 cikin 109 da ke wakiltan mazabu dabam dabam a fadin kasa Najeriya.