Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna sun ceto ‘yan Kasar Jamus din nan biyu da barayi sukayi yi garkuwa da su a kudancin jihar Kaduna.
Wadanda akayi garkuwar da su dai sun dade a yanki suna nazarin tarihin mutanen yankin wanda ya hada da dadadden tarihin mutanen NOK.
Wani jami’in rundunar ‘yan sandan jihar ya ce an ceto ‘Yan kasar Jamus din ne Peter Breunig da Johannes Buringer batare da an biya ko anini ba duk da cewa wadanda sukayi garkuwan dasu sun nemi da abasu kudade kafin su sakesu.
An sako su a daren jiya Asabar ne.
Ranar larabar da ta wuce ne akayi garkuwa da ‘yan kasara jamus din su biyu a garin Jenjere da ke masarautan Kagarko, Kudancin jihar Kaduna.