Jiya Asabar ne Allah yayi wa mahaifiyar sarkin Katsina Hajiya Aminatu Mai Babban daki rasuwa.
Ta rasu ne bayan tayi fama da rashin lafiya sannan ta bar ‘ya’ya tara cikin su sarkin Katsina
Abdulmumini Kabir Usman.
Za’ayi jana’izan Hajiya Aminatu yau lahadi a Katsina.