Ali Modu Sherrif ba matsala bane – Inji Walid Jibril

0

Shugaban kungiyar amintattun jam’iyyar PDP, Walid jibrin yace hukuncin da kotu ta yanke na tabbatarwa Ali Modu Shareef kujeran shugabancin Jam’iyyar PDP bai da’da su da kasa ba ko kadan.

Walid Jibrin ya fadi hakanne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja bayan hukuncin da kotu ta yanke akan wanene ya kamata ya shugabanci jam’iyyar PDP din tsakanin Tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmed Makarfi da Sanata Ali Modu Sherrif.

Walid ya kara da cewa jam’iyyarsa za ta warware duk matsalolinta sannan kuma tana nan ta na ganawa da sauran ‘ya’yan jam’iyyar wanda suke tare har yanzu da wanda basa tare domin dinke duk wata Baraka da take jam’iyyar a yanzu.

Yace komai zai canza kuma sune za suyi dariya daga karshe.

Share.

game da Author