Gwamnan jihar Barno Kashim Shettima yace akalla mutane 100,000 suka rasa rayukansu a sanadiyyar hareharen Boko Haram a jihar Barno kamar yadda bayanai daga kauyukan jihar suka nuna.
Kashim Shettima ya fadi hakanne a lokacin da yake bada bayanai akan barnan da Boko Haram tayi a jihar a wajen taron tunawa da Janar Murtala Mohammed da akayi a gidan tunawa da Shehu Musa ‘Yar Adua da ke Abuja.
Gwamnan yace sama da mutane miliyan biyu ne suka rasa muhallinsu a sanadiyyar hare-haren Boko Haram.
Yace mutane 537,815 suna zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira dake fadin jihar.
Akwai wasu kuma’yan gudun hijira dasuke zaune a sansanonin dake garuruwan Ngala, Monguno, Bama, Banki, Pulka, Gwoza, Sabon Gari.
Bayan haka akwai mutane 73,404 da sukayi gudun hijira zuwa kasashen Kamaru da Nijar. Mutane 11,402 na kasar Nijar wasu kuma 62,002 na kasar Kamaru.
Akwai marayu 52,311 sannan kuma matan da suka rasa mazajensu su 54,911.
Mutane 9,012 sun koma garuruwansu dake kananan hukumomin Ngala, Monguno, Damboa, Gwoza da Dikwa.