Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo yace sun dauki tsawon lokaci suna hira da shugaban kasa Muhammadu Buhari ta wayar tarho daga kasar Ingila yau.
Osinbajo yace kamar yadda yaji a tattaunawarsu Buhari na nan cikin koshin lafiya da annashuwa.
Yace zama ne ya kama shi a kasar Ingila domin akwai wasu gwaje-gwajen lafiyarsa da zai yi kamar yadda likitoci suka shawarceshi.
Yace bayan tattaunawa da sukaya akan Kasafin kudin 2017, sun yi mana akan tattalin arzikin kasa da kuma inda aka tsaya akan hakan bayan tafiyarsa.
Da aka tambayeshi wai akwai rade-radin cewa wai wasu na tilasta masa da ya sauka daga kujeransa na mataimakin shugaban kasa, Osinbajo yace wannan hira ce kawai amma hakan ma ba zai yiwu ba domin ai zaben sa akayi saboda haka tayaya haka kawai zai sauka daga kan kujeransa na mataimakin shugaban kasa.
Daga karshe yace shugaban kasa zai dawo kasa Najeriya da zaran ya kamala gwaje-gwajen lafiyasa.
Discussion about this post