Abun da Trump ya fada wa Buhari ta wayar Tarho

1

Fadar shugaban kasar Amurka ta tabbatar da wayar da shugaban Kasar Donald Trump yayi da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Gidan Jaridar PREMIUM TIMES ta samu bayanai akan hakan daga ofishin harkokin kasashen Afrika da ke kasar Amurka domin samun cikakkun bayanai akan tattaunawar shugabannin biyu.

Ofishin ta tabbatar da wannan tattaunawa sannan ta ba da bayanani akan abubuwan da Trump da Buhari suka Tattauna akai.

A bayanan, Trump yace a shirye yake da ya taimaka wa Buhari da duk wata taimako da yak e bukata domin samun nasara akan yaki da Boko Haram da gwamnatinsa ta keyi ta hanyar siyar wa kasa Najeriya da Jiragen yaki na sama.

Yace kasar Amurka zata taimakawa Najeriya wajen farfado da tattalin arzikin kasarta da kuma mara mata baya akan shugabancin da ta ke bada wa kasashen nahiyar Afrika.

Daga karshe ya jinjina wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan shugabanci nagari da yake a kasa Najeriya da yi masa fatan Alkahiri a tsawaon mulkinsa.

Karanta labarin a shafin mu na turanci a nan: http://wp.me/p2LdGt-Wbm

Share.

game da Author