Wani mazaunin garin Kubwa da ke babban birnin tarayya, Abuja ya maka uwargidansa a wata kotu da ke yankin saboda tana gamsar da sha’awarta ta hanyar yin amfani da hannayenta.
“Na kamata sau dayawa tana wasa da gabanta da hannayenta a daki, na kwabe ta da ta daina amma taki dainawa gashi yanzu har ta harbi ‘Yar mu dashi.”
Magidancin mai suna Ekpolador Ebi, ya fadi hakanne a lokacin da yake rokon kotu ta raba aurensa da matarsa mai suna Gloria Onajero.
Ya roki kotu da ta warware auren su saboda irin wadansu dabiu da matarsa takeyi da bai gamsu dasu ba sannan kuma ya na zarginta da yawon ta zubar.
Duk da Allah ya albarkace su da ‘ya’ya biyu da Gloria, Mai gidan nata na zargin cewa ‘ya’yan ba nashi bane, Kuma abubuwan da takeyi yana bata tarbiyya da dabi’un ‘ya’yan.
Tana gamsar da shawarta ta hanyar yin amfani da hannayenta inda a yanzu hakan babban ‘yar su ta fara aikata hakan.
Ya kuma roki kotu da ta kwato masa dukiyarsa da ke hannun ta sannan kuma ta ja mata kunne akan yadda take lakada wa ‘ya’yansu duka babu gaira babu dalili.
Alkalin Kotun Bello Kawu ya daga karan har zuwa 21 ga watan maris domin ci gaba da saurare.