Kwamishanan kiwon lafiyar jihar Nasarawa Daniel Iya ya sanar da mutuwan mutane 4 da suka kamu da cutar zazzabin lasa a jihar.
Mr Daniel ya sanar cewa da ma akwai wasu mutane 16 dake fama da cutar kuma daga cikin su ne 4 suka rasa rayukansu.
Mr Iya ya ce bincike ya nuna cewa 3 daga cikin mutanen 4 da suka rasu ‘yan uwa ne kuma suna zama wuri daya kuma ma’aikatarsa na gwada mutane 36 wanda suke zargin sun yi muamula da su domin hana yaduwar cutar.
Ya kuma ce sun hada karfi da karfe da gwamnatin tarayya wajen samarda kayan aiki kamar magunguna, naurorin gwaji da kuma kara wayar da kan malaman asibiti aka illolin yaduwar cutar.
Ya kuma kara fadakarwa malaman asibitin akan mahimmanci yin gwaji wadda zai taimaka wurin gano cutar da sauri kafin su fara bada magani.
Daga karshe ya shawarci mutane da su yi kokarin zuwa asibiti muddun su ka kamu da zazabi.