Tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shema ya bayyana yau a gaban wata kuto da take zamanta a garin Katsina.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta gurfanar da shi akan zarge-zargen cin hanci da rashawa da yin sama da fadi da kudaden jihar lokacin da yake gwamnan Jihar.
Hukumar EFCC na zargin Ibrahim Shema ne da wadansu su uku da laifin karkatar da kudin da ya kai Naira biliyan 11 na kananan hukumomin jihar.
Ta roki kotu da ta yaddar mata ta rike Shema har sai ta gama bincike akan abubuwan da ake zarginsa akai.
Lauyan Shema, Joseph Daudu ya ce kotun ba ta da hurumin sauraron karar ganin yadda aka shigar da ita ba tare da an bi cikakkun ka’idojin shigar da kara irin wannan ba.
Sannan yayi kira ga kotun da ta yi watsi da maganar rike tsohon gwamnan saboda rashin inganci da karar ke dashi.
Kotun ta amince da hakan sannan ta daga Karan zuwa 7 ga watan Fabrairu domin cigaba da sauraro.
Domin guje ma irin hakanne a watan Satumbar 2016 Ibrahim Shema ya kai kansa hukumar ta EFCC bayan hukumar ta yi sanarwan bukatarsa da ya ziyarce ta domin amsa tambayoyi.