Gwamnan jihar Kaduna, Mal. Nasir El-Rufai yace gwamnatinsa ba za tayi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wani da aka kama da hannu a rikicin Kudancin Kaduna.
El-Rufai ya fadi hakanne yau a garin Kaduna a lokacin da kwamitin Majalisar dattijai ta ziyarce shi a fadar gwamnatin jihar.
Gwamnan ya kara da cewa tsawon shekara 35 kenan ana samun ire-iren wadannan rikice-rikice a jihar Kaduna amma har yanzu babu wani mutum daya da akace wai an kama kuma an hukunta shi.
Ya kara da cewa yanzu jihar Kaduna rabe take saboda rashin zaman lafiya.
An nada Kwamitin ne domin su binciko ainihin musabbabin rikicin sannan su bada shawara akan sakamakon binciken nasu wa majalisar dattijai domin tattaunawa akai.
Sanata Kabiru Gaya da ga jihar Kano ne yake jagorantar kwamitin.
Da yake na shi jawabin, Kabiru Gaya ya yi kira ga ‘yan siyasa da su guji yin amfani da siyasa wajen tada zaune tsaye.
Yace kwamitin za ta kai ziyara kauyukan da tashin hankalin ya faru sannan kuma zasu tattauna da mutanen yankin da rikicin yaki ci yaki cinyewa.