Shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki ya ce da zaran sun dawo daga hutu za su fara bincike akan rikicin Kudancin Kaduna.
Saraki ya fadi hakanne a shafin sadarwansa na twitter.
Ya ce zasu binciki kashe kashen da ake zargin anyi a rikicin.
Wani fasto mazaunin yankin ya ce akalla mutane 800 ne suka rayukansu a rikicin yankin.