Za mu maka gidan Jaridar PREMIUM TIMES a kotu saboda samun bayanai da sukayi akan rundunar sojin Najeriya

0

Kakakin rudunar sojin Najeriya SK Usman yace fadan babban hafsan sojin Najeriya da gidan Jaridar PREMIUM TIMES da bam da wanda rundunar sojin za ta shigar kotu akan gidan jaridar.

SK Usman yace rundunar sojin za ta maka wannan gidan jarida a kotu saboda amfani da wadansu takardu da ta samo wajen rubuta labaran ta akan mayakan sojin Najeriya wanda a cewarsa bata da hurumin samun wadannan bayanai.

Ko daya ke kakakin rundunar sojin bai amabato ko wasu takardu bane suke korafi akai yace za su je kotu domin ganin wannan gidan jarida ta ba da bayanai akan hakan.

Ko da yake rundunar sojin sun nisan tar da kansu inda suka dangana samamen da aka kai kamfanin PREMIUM TIMES ga babban hafsan sojin Najeriya Tukur Burutai sun manta cewa da takardu dauke da tambarin rundunar sojinne akayi ta amfani dasu wajen sakonnin da aka turo gidan Jaridar akan tuhumar labaran da su ka ce wai ya ingiza shi Burutai din.

Shugaban wannan gidan Jarida, Dapo Olorunyomi yace gidan jaridar na nan a bakanta na bin dokokin aikin jarida kafin ta wallafa duk wani labari da zai fito daga wannan kafa nata.

Share.

game da Author