Shugaban kamfanin gidan jaridar PREMIUM TIMES Dapo Olorunyomi ya fadi dalilan da ya sa jami’an tsaro suka Kai wa kamfanin Samame ranar Alhamis din da ya gabata.
A hiran da yayi gidan jaridan Talabijin na Oak, Dapo ya ce dalilin samamen da jami’an tsaron suka kawo ma kamfanin inda aka tafi da shi da kuma wata ma’aikiciyar kamfanin yana da nasaba ne da wata labarin da gidan jaridar ta rubuta sannan ta wallafa akan shugaban sojin Najeriya Tukur Buratai akan zargin cin hanci Wanda wata kungiyace mai suna CSNAC ta nemi hukumar kula da da’ar ma’aikata CCB da ta binciki hakan.
Ko da yake hukumar kula da da’ar ma’aikatan ta ce ba za ta Iya bincike da sauraron wannan zargi da tuhuma da akeyi akan babban hafsan sojin kasan Najeriya din ba saboda aikin da yakeyi ba na Samar da zaman lafiya a yankin Arewa maso gabas da yaki da Boko Haram ba kamar yadda kungiyar CSNAC ta bukata hukumar Soji ta musanta hakan.
Dapo yace bayan wannan rahoto da wannan gidan jarida ta wallafa ne sai hukumar sojin Najeriya ta fusata akan wannan labarin inda ta nemi kamfanin PREMIUM TIMES ta cire labarin daga shafinta na yanar gizo kuma ta roki sojin Najeriya gafara akan wallafa wannan labari ko kuma ta maka gidan jaridar a kotu.
Bayan hakane Gidan jaridar Premium Times ta ce ba za ta rokesu gafara ba sannan ba za ta cire wannan labari ba musamman ganin cewa ta rubuta shi ne akan dukkan sharuddan daya kamaci rubuta kowani irin labari a aikin jarida.
Toh shine fa suka fusata ba tare da yin isasshen bincike akan hakan ba kwai suka Kawo samame kamfanin inda suka tafi da shi shugaban da Evelyn Okakwu.
Bayan takaddama da akayi tsakanin kamfanin jaridar da Kai ruwa Rana da akayi da ‘yan sandan da suka kamasu, awowi bayan haka sai aka sako su.
Babban editan gidan jaridar PREMIUM TIMES Musikilu Mojeed ya ce cin zarafi da kuma yin barazana da akayi wa wannan gidajen jaridar bai kamata ba kuma yace jaridar zata cigaba da aikinta na zage gaskiya domin yin biyayya da sanar masoyan wannan gidan jarida da mutanen Najeriya gaskiya akan abubuwan da ya ke faruwa a kasa Najeriya.