Ministan yankin Neja-Delta Usain Usain ya ce a watan Fabrairu mai zuwa gwamnatin tarayya za ta aiko wasu kwararrun likitoci domin duba marasa lafiya a yankin.
Ministan Ya fadi hakan ne a wata hiran da yayi da kamfanin dillancin labarai.
Ya ce ma’aikatarsa da kungiyar likitocin da suka kware a fidar cutar dake kama gaban mace da namiji ne su ka dauki nauyin gudanar da irin wannan aiki ga mutanen yankin kyauta.
Ministan ya ce za’ayi hakanne domin samarwa mutanen yankin kula ta musamman akan lafiyarsu ganin cewa kasa Najeriya na amfana da arzikin da Allah ya ba wannan yankin.
Ko da yake ministan bai fadi asibitocin da za su fara aikin ba amma ya ce lallai hakan zai taimakawa mutanen yankin musamman wadanda suke karkara.
Bayan hakan kuma ya yi bayanin cewa ma’aikatarsa ta hada hannu da wadansu likitoci domin su zo su duba mutanen yankin akan cututtukar da ya shafi na hawan jinni, cutar siga, cutar zazabin cizon sauro, cutar kanjamau da kuma bada magunguna akai.