A sanadiyyar ayyukan ‘yan kungiyar Boko Harama yankin arewa maso Gabas, Shekara biyu kenan wadansu daga cikin mazauna garuruwan yankinsuke zaune a wasu sansanonin ‘yan gudun hijira dake fadin Kasarnan. Daya daga cikin sansanin shine wanda yak e kauyen Wasa dake babbabn birnin tarayya Abuja.
A yadda shirin yake ya kamata ace wuraren zaman nasu ya za mo musu wajen da zasu sami natsuwa da kwanciyar hankali sai gashi dalilin rashin kula har rayuka ake rasawa a sansanoni.
Rilwanu Mohammed, Babban Sakataren cibiyar kula da lafiya na matakin farko na babban birnin tarayya y ace akalla yara 10 ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar cutar kwalera, wato Amai da gudawa a sansanin Wasa da ke yankin Apo, Abuja.
Wata mazauniya sansanin Wasa, Elizabeth Ibrahim wanda ta rasa danta mai suna Musa a sanadiyyar barkewar annubar a sansanin ta ce ta rasa daya daga cikin ‘ya’yan ta ne Musa dan shekara 7 tare da wadansu a dalilin cutar na amai da gudawa da ya afka wa sansanin.
Ta kuma ce ba wannan ba shine ne karo na farko da sansanin ke fuskantar irin wannan annobar ba domin cutar ta kashe ‘ya’ya 6 a shekarar 2015.
RASHIN RUWA
Elizabeth Ibrahim ta ce sun yi matukar wahalar samun ruwan sha a sansanin kafin wata kungiya mai zaman kanta gina musu rijiyan burtsatse kuma suna siyan ruwan a jarka a kan Naira 10.
Ta ce sukan yi doguwar tafiyar na tsawon kilomita masu yawa domin debo ruwan da za suyi amfani da shi a wata rafi dake alkaryar.
‘Yan gudun hijiran sun koka da yadda gwamnatin Najeriya ta kyalesu suke ta wahala sannan basu ga wani taimako da gwamnati take kawo musu ba domin warware musu matsalolin da suke fama dashi a sansanin.
Ko da yake Gwamnati ta umurcesu da su koma garuruwansu inda hakan ba zai yiwu ba saboda irin bayanan da suke samu akan cewa haryanzu Boko Haram basu daina kai hare-hare garuruwan ba.
RASHIN ASIBITI
A dalilin rashin Asibiti a sansanin ‘yan gudun hijira da ke kauyen Wasa Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ne ya gina wata karamar asibiti tun watar Maris amma har yanzu ba ta fara aiki ba.
Mohammed ma’aikacin kiwon lafiya na matakin farko yace har yanzu ba a ba ma’aikatarsa na kiwon lafiya ba ikon bude Asiitin domin su fara aiki.
Mustapha Abdulkareem na karamar hukumar AMAC yace ta turo likitoci zuwa sansanin wanda zai kula da kiwon lafiyan ‘yan gudun hijiran.
Akan matsalar rashin ruwa mai tsafta a cikin sansanin, Wani Jigo a gidauniyar ‘Water Aid’ Oluwaseyi Abdulmalik ya roki ma’aikata da ‘yan gudun hijiran da ke sansanin da su yi kokarin tsaftace muhallin su domin gujewa cutar amai da gudawa.