‘Yan Shi’a sun fito da yawansu domin yin zanga-zanga akan yadda gwamnati ta nuna halin ko inkula ga shugaban kungiyar Ibrahim El-Zakzaky duk da cewa kotu ta yanke hukunci da gwamnati ta sako shi.
Gwamnati ta tsare shugaban kungiyar Ibrahim El-Zakzaky bayan arangamar da kungiyar tayi da sojojin Najeriya a garin Zariya.
An gudanar da Zanga-Zangar a garuruwan Kaduna,Katsina,Sokoto,Kano da kuma birin tarayya Abuja. Yan kasar Najeriya a kasar Iran suma ba a barsu a baya ba domin sunji ofishin jakadancin Najeriya dake Tehran domin bada nasu gudunmawar.