‘Yan banga da jami’an tsaro sun dakile wata hari a kauyukan Usmanti da Kaleri

0

Jami’an tsaro da ‘yan banga sun dakile wata hari da aka kai wa jami’an tsaron a unguwannin Usmanti da Kaleri dake karamar hukumar Mafa, jihar Borno.

Mabiya Kungiyar Boko Haram ne suka kai wannan hari

Maharan dauke da bamabamai sun kai farmakin ne a daren jiya talata inda wadansu jami’an tsaro suka hango su sannan kafin su tada bam din suke harbe su.

Na biyun kuma ya faru ne a dai dai lokacin da ake gudananr da sallar Asuba na ranar Laraba inda kafin su isa masallacin suka ta da bam din.

Maharanne suka mutu inda mutum biyu daga cikin ‘yan bangan suka sami raunuka.

Daya daga cikinsu ya rasa ransa.

Share.

game da Author