Tsohon shugaban kasar Najeriya Abdussalami Abubakar yace ya kamata ayi takatsantsan da maganar rikicin kudancin Kaduna tun kafin ya zama wani abu da bam.
Ya fadi hakanne a wata ziyara da ya Kai garin Kaduna tare da Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad, Rebaren Hassan Kuka domin nuna rashin jin dadinsu da abubuwan da yake faruwa a yankin kudancin Kadunan.
Ya ce sun zo Kaduna ne ne domin su gani ma idanuwarsu sannan su roki jama’a da a zauna lafiya da juna.
Ya ce zasu ziyarci yankin kudancin Kadunan sannan zasu tattauna da mazauna garuruwan da kuma sarakunan yankin Inda bayan hakan za su gana da gwamna El-Rufai domin bashi nasu shawarwarin akan yadda za’abi a sami tabbataccen zaman lafiya a jihar baki daya.
Yanzu dai zaman lafiya ya dawo a yankin kudancin Kadunan sannan gwamnati ta Kara tsaurara matakan Tsaro a yankin da jihar baki daya.