Wani direban motar haya Mr Akangbe ya banka wa dansa mai suna Sola wuta saboda sata da yayi a garin Omu-Aran da ke jihar Kwara.
Sola dai ya rasa ransa a dalilin hakan.
Kotun da ta saurari shari’ar karan a garin ta yanke wa Mr Akanbi hukuncin kora daga wannan gari kwata-kwata kuma ta bashi mako daya da ya tattara inashi-inashi ya bar garin saboda mummunar aikin da ya aikata.
Ko da yake wannan dabi’a na Sola ba farau ba, an taba ceto sa daga irin hakan a kwanakin baya inda Mr Akangben dai ya nemi ya halakashi da wuta ta hanyar kona shi.
Kotun yace abin da mahaifin Sola ya yi bai dace ba kuma ya karya dokar jihan inda hakan ya sa kotun ta sanar da ‘yan uwan mahaifin Sola wanda suke garin Isanlu-Isin akan abin da ya faru da kuma hukuncin da suka yanke.
Ya kuma yi amfani da wannan damar domin ya gargadi sauran ‘yaran da suke aikata munanan ayyuka irin wannan da su yi hattara domin za a hukunta duk wanda aka kama ya aikata irin wannan laifi.