Umarni daga sama ya sa muka kai samame gidan jaridar PREMIUM TIMES – Hukumar ‘Yan sanda

0

A yammacin Alhamis ne ‘yan sanda suka kawo samame ofishin gidan jaridar PREMIUM TIMES da ke Abuja inda suka yi waon gaba da wadansu ma’aikatan kamfanin da ya hada da Shugaban kamfanin Dapo Olorunyomi da kum wata Evelyn Okakwu.

Bayan kai ruwa rana da akayi tsakanin shugabannin kamfanin da Lauyoyinsu a shelkwatan hukumar ‘yan sanda dake Abuja an sako ma’aikatan gidan jaridar sannan an umurcesu da su koma ofishin da safen Juma’a.

Kakakin hukumar ‘yan sanda Don Awunah ya fada wa gidan jaridar Premium Times cewa dalilin da ya sa ‘yan sandan suka kai wannan samame ofishin Premium Times din shine domin karan da lawuyoyin babban hafsan sojin kasan Najeriya Tukur Buratai yakai gaban su ya na kara akan cin fuska da gidan jaridar tayi masa a wani labarin da ta rubuta.

Wani babban jami’in ‘yan sanda ya sanar ma wannan gidan jarida cewa abinda hukumar na ‘yan sanda suke so shine su sami dama da ga kotu domin daure shugaban kamfanin da ma’aikaciyarsa.

A yanayin da ake ciki, kamun da ‘yan sandar suka yi ya janyo tsokaci daga masa da kungiyoyin kare hakkin dan Adam kamarsu AMNESTY INTERNATIONAL da na kare hakkin ‘yan jarida akan irin wannan cin fuska da ‘yansanda suke ma musamman yan jarida da wanda sukayi jiya akan ma’aikatan gidan jaridar PREMIUM TIMES.

Kungiyar da ke kare hakin ‘yan jarida ta duniya, CPJ ta yi gargadi ga hukumomin Najeriya da su daina yin barazana ga ma’aikatan gidan jarida a kasar.

Wakilin CPJ a yankin Afrika ta yamma Peter Nkanga ya ce kamun da ‘yan sandan suka yi wa ma’aikatan gidan jaridar ya nuna cewa jami’an tsaro na da wata kullalliya akan akan gidan jaridar mussam yadda ta ke tsaga gaskiya a labarunta.

Sanata Shehu Sani yace irin haka ya faru da mawallafi gidan jaridar sahara Reporters Omeyele Sowore. Ya kuma ce cigaba da yin hakan na nuna yadda kasar ke neman koma wa mulkin kama karya wanda aka fi sani da mulkin sojoji.

Wasu marubutan jarida kamar su Kadaria Ahmed,Pius Adesanmi, Okey Ndibe da Sonala Olumhense sun rubuta wasika ta musamman zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari akan cin zarafin da hukumomin tsaro sukayi wa gidan jaridar PREMIUM TIMES sannan suka rokeshi da ya ja ma jami’an tsaro kunne akan hakan.

Share.

game da Author