Tsohon ministan kwadugo ya koma jam’iyyar APC

0

Wani tsohon ministan kwadigo Joel Ikenga kuma jigo a jam’iyyar PDP ya canza sheka daga jam’iyar zuwa jam’iyar APC.

Joel ya sanar da hakanne da yake ganawa da manema labarai ranar Litini a jihar Taraba.

Ya yi bayanin cewa dalilin sauya shekar nasa shine domin ganin irin nasarori da kyawawan ayyuka da wannan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ke ta aiwatarwa tun daga lokacin da ta hau karagar mulki.

Bayan haka kuma ya ce ya gamsu da yaki da cin hanci da rashawa da wannan gwamnati ta sa a gaba.

Tsohon minista Joel ya kara da cewa cikin dalilan da ya sa ya fice daga jam’iyyar PDP shine domin nasarorin da aka samu wajen yaki da kungiyar Boko Haram da kokarin dawo da zaman lafiya a yakin arewa maso Gabas.

Domin haka ya shawarci ‘yan Najeriya musaman wadanda suke yakin arewa maso gabas da su mara ma gwamnatin baya domin babu yankin da ta fi amfana da ayyukan mulkin Buhari kamar yankin arewa maso gabas.

Daga karshe tsohon ministan ya ce zai ci gaba da mara ma gwamnatin baya domin samin nasarori akan abubuwan da ta sa a gaba.

Share.

game da Author