Tattaunawa ne kawai zai sa a samu zaman lafiya a kudancin Kaduna – Gwamna Lalong

0

Gwamnan jihar Filato Simon Lalong yace dolene shugabannin addinai da na gargajiya dake yankin kudancin Kaduna su dawo a hadu a taburin sulhu domin samun zaman lafiya dawwamammiya a yankin.

Ya kuma shawarci gwamnan jihar Kaduna da ya yi kokarin ganin an hukunta duka wanda aka samu da hannu a rikicin domin ya zama ishara ga na baya.

Gwamna Lalong fadi hakanne a wata wasikar ta’aziyya da ya aika wa gwamnan jihar Kaduna domin yin jaje akan abinda ya faru a kudancin jihar Kadunan.

Ya ce gwamnatin jihar Filato za ta taimaka wa jihar Kaduna musamman idan bukatar hakan ya taso.

Ya roki jama’a da a zauna lafiya da juna domin samun cigaba mai dorewa.

Share.

game da Author