Jirgin saman sojin Najeriya ta harba bam a sansanin yan gudun hijira dake Rann a karamar hukumar Kala-balge, jihar Borno.
Harin dai an kaishi ne cikin kuskure.
Daruruwan mazauna sansanin ne suka samu raunuka inda aka tabbatar da rasuwan mutane 2.
Jami’in Sojin Najeriya Rabe Abubakar ya tabbatar da hakan in da yace lallai hakan ya faru ne cikin kuskure.
Cikin wadanda suka sami raunuka har da ma’aikata bada agaji na MSf da ICRI.