Shugabannin Addinai na daga cikin wadanda suke rurura wutan rashin zaman lafiya a yankin Arewa

2

Sarkin Musulmi kuma shugaban sarakunan Arewacin Najeriya Dr Abubakar Sa’ad yayi kira ga kungiyoyin addinan kasar nan da su daina amfani da addini wajen ingiza mabiyansu wajen tada zaune tsaye.

Dr Sa’ad ya fadi hakanne a taron da akayi a garin kaduna na gwamnoni da shugabannin yankin arewacin Najeriya din domin samo mafita akan rikicin kudancin Kaduna.

An gudanar da taron ne a dakin taro na gidan tunawa da Hassan Katsina da ke Kaduna.

Ya kara da cewa sarakunan yankin arewacin Najeriya din zasu mara ma gwamnonin yankin akan duk wata shawara da za su dauka akan yadda za’ayi a kawo karshen irin wannan tashin hankali.

Shuagaban kungiyan gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yace talauci da jahilci shine yayi mana katutu a yankin arewa wanda hakan yasa yankin kudancin kasar nan su kayi mana zarra.

Yace dole ne a matsayinsu na gwamnoni su nemo duk wata hanya da za’a magance irin wadannan fitunu a yankin.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi kira ga Sarakuna da su sani cewa sun fi kusa da jama’a kuma sune hakkin seta rayuwar jama’arsu yake kansu.

Gwamnonin da sarakunan Arewacin Najeriya ne suka halarci taron da ya gudana yau litinin a garin Kaduna.

Share.

game da Author