Shakuwata da Nafisa, Rahama bai wuce na aiki ba – Inji Hafsat Idris

1

A farfajiyar finafinan Hausa wato Kannywood mutane da yawa suna ganin ‘Yarwasa Hafsat Idris a matsayin sabuwar ‘yarwasa amma kuma ita jaruma ce domin tun da ta fito a wata fim mai suna Barauniya ta zama babbar Jaruma saboda hazakar da ta nuna a fim din.

Gidan jaridar PREMIUM TIMES ta yi hira da Hafsat Idris yayin da take daukar wata sabuwar fim mai suna ‘Gimbiya Sailuba’ a garin Abuja.

Da aka tambayeta akan daukakar da ta samu na faraddaya a harkar fim, Hafsat tace “Ikon Allah ne kawai da kuma himma da na sa akan sana’ar saboda ban taba irin wanan aikin ba amma tun da ta fara fitowa a fina-finan Hausa gaba na ke ta yi kuma ina wa Allah godiya da kuma kamfanin Maikwai Records da ta fara saka ni a fim.

Ta kuma ce za ta so ta cigaba da aikin fina-finan Hausa duk da cewa aure ne ke gaban ta a yanzu haka.

“Kwarai da gaske ina da saurayin da na ke matukar so sai dai ba dan fim bane.”

Bayan haka kuma Hafsat Idris ta bada bayani akan dangartakarta da Jarumai Nafeesa Abdullahi da Rahama Sadau da kuma a me zata fito a wasan ‘Gimbiya Sailuba’’

” Dangartakana da Rahama da Nafeesa ba ya wuce a wurin aiki. Idan aiki ya had mu zamuyi tare cikin fara’a da nishadi amma bayan haka babu wata alakar kawance da ke tsakani na da su.

A cikin Fim din Gimbiya Sailuba kuma, Hafsat tace za ta fito ne a matsayin gimbiya, san kowa kin wanda tya rasa.

Share.

game da Author