Babban darektan hukumar kula da asibitocin jihar Borno wato ‘Borno state Hospital Management Board BSHMB’, Salisu Kwayabura ya ce gwamnatin jihar Borno ta kashe makuden kudi domain gyaran manyan asibitoci 38 da Boko Haram ta lalata a hare haren ta.
Ya yi bayanin cewa sun yi haka ne domin tabbatar da ‘yan jihar musamman mata uwaye da kuma yara sun sami ingantacciyar kiwon lafiya a jihar da kuma wadata asibitocin da kayayyakin aiki sannan ta karo ma’aikatan kiwon lafiya 4,300 domin samun nasara akan hakan.
Salisu yace sun karo likitoci 158, malaman asibiti da kuma unguwar zoma 1094, masu bada agaji 29, masu bada magani wato ‘Pharmacists’ a turance 12 da kuma sauran su.
Ya Nuna bakin cikinsa akan irin dinbin hasarar da ayyukan Boko Haram yayi ma jihar musamman ta fannin kiwon lafiya.
Daga karshe ya yi bayanin cewa gwamnatin jihar Borno ta gina cibiyar kiwon lafiyar mai gadajen kwanciya guda 250 domin uwaye mata da kuma kananan yara ‘yan shekara 1 zuwa 5 a jihar.