Wannan shine karo na biyu da gwamnatin jihar Kaduna za ta saka dokar hana fita na awoyi 24 a karamar hukumar Zangon Kataf.
Gwamnati ta sanar da hakanne a wata sanarwa da Kakakin gwamnan jihar Samuel Aruwan ya sanya ma hannu.
Yace dalilin saka dokar shine barkewar wata rikici a garin Samarun-Kataf inda matasa suka afka ma shagunan mutane a wata kasuwa da yammacin yau.
Gwamnatin jihar ta saka dokar hana fita, da zirga-zirga a karamar hukumar, ta ce kowa ya zauna a gidansa.